Waƙoƙin Sarewa da Ganga

Tatsuniyar da ke bayyana ’yancin addini ko imani.

Tatsuniyar da ke bayyana ’yancin addini ko imani

‘Waƙoƙin Sarewa da Ganga’ tatsuniya ce da ke taimaka wa mutane su yi tunani kan ko suna daraja haƙƙoƙin da ’yancin addini ko imani ke karewa.

Ya dace matuƙa wajen taimaka wa yara, matasa da manya su bincika ra’ayoyinsu game da wannan haƙƙi ba tare da yin magana kai tsaye a kansa ba — wanda hakan ke sa ya zama musamman mai amfani a yanayi masu wahala.

Idan kana aiki da matasa da manya, za ka iya amfani da wannan tatsuniya tare da atisayen tattaunawa mai taken ‘Da can, a wani lokaci’, wanda ke cikin Koyarwar Masu kawo Sauyi na Asali (manhajarmu don wayar da kai da kuma motsa al’umma a matakin ƙasa).

A wannan shafi za ka iya sauke labari, fastoci masu ɗauke da zane-zanen hoto, fayil na PowerPoint mai ƙunshe da hotunan tare da rubutun a cikin bayanan mai gabatarwa, da kuma takardar rabawa don atisayen tattaunawa.

“Aikin ‘A wani lokaci a can baya’ ya haifar da muhawarori masu zurfi sosai. Ya bude tagogi da dama a cikin tunanin mutane. Sun fara yin tunani a kan al’ummominsu – daga dokokin jinsi, ko yana da kyau a karya tsoffin al’adu da sukayi katutu.”

Hammam Haddad

Mai shirya koyarwar, Jordan

Ƙara wayar da kan mutane game da ’yancin addini ko imani a cikin al’ummarku

Gano Koyarwar Masu kawo Sauyi na Asali

Danna nan